المص(1) A. L̃. M̃. Ṣ̃. |
كِتَابٌ أُنزِلَ إِلَيْكَ فَلَا يَكُن فِي صَدْرِكَ حَرَجٌ مِّنْهُ لِتُنذِرَ بِهِ وَذِكْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ(2) Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai. |
اتَّبِعُوا مَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ وَلَا تَتَّبِعُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ ۗ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ(3) Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa. |
وَكَم مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا فَجَاءَهَا بَأْسُنَا بَيَاتًا أَوْ هُمْ قَائِلُونَ(4) Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla. |
فَمَا كَانَ دَعْوَاهُمْ إِذْ جَاءَهُم بَأْسُنَا إِلَّا أَن قَالُوا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ(5) Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci," |
فَلَنَسْأَلَنَّ الَّذِينَ أُرْسِلَ إِلَيْهِمْ وَلَنَسْأَلَنَّ الْمُرْسَلِينَ(6) Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin. |
فَلَنَقُصَّنَّ عَلَيْهِم بِعِلْمٍ ۖ وَمَا كُنَّا غَائِبِينَ(7) Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba. |
وَالْوَزْنُ يَوْمَئِذٍ الْحَقُّ ۚ فَمَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ(8) Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara. |
وَمَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُم بِمَا كَانُوا بِآيَاتِنَا يَظْلِمُونَ(9) Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci. |
وَلَقَدْ مَكَّنَّاكُمْ فِي الْأَرْضِ وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ ۗ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ(10) Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa. |
وَلَقَدْ خَلَقْنَاكُمْ ثُمَّ صَوَّرْنَاكُمْ ثُمَّ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ لَمْ يَكُن مِّنَ السَّاجِدِينَ(11) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba. |
قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلَّا تَسْجُدَ إِذْ أَمَرْتُكَ ۖ قَالَ أَنَا خَيْرٌ مِّنْهُ خَلَقْتَنِي مِن نَّارٍ وَخَلَقْتَهُ مِن طِينٍ(12) Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka." |
قَالَ فَاهْبِطْ مِنْهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَن تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَاخْرُجْ إِنَّكَ مِنَ الصَّاغِرِينَ(13) Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci." |
قَالَ أَنظِرْنِي إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ(14) Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su." |
قَالَ إِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَ(15) Ya ce: "Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri." |
قَالَ فَبِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأَقْعُدَنَّ لَهُمْ صِرَاطَكَ الْمُسْتَقِيمَ(16) Ya ce: "To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici." |
ثُمَّ لَآتِيَنَّهُم مِّن بَيْنِ أَيْدِيهِمْ وَمِنْ خَلْفِهِمْ وَعَنْ أَيْمَانِهِمْ وَعَن شَمَائِلِهِمْ ۖ وَلَا تَجِدُ أَكْثَرَهُمْ شَاكِرِينَ(17) "Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba." |
قَالَ اخْرُجْ مِنْهَا مَذْءُومًا مَّدْحُورًا ۖ لَّمَن تَبِعَكَ مِنْهُمْ لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمْ أَجْمَعِينَ(18) Ya ce: "Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya." |
وَيَا آدَمُ اسْكُنْ أَنتَ وَزَوْجُكَ الْجَنَّةَ فَكُلَا مِنْ حَيْثُ شِئْتُمَا وَلَا تَقْرَبَا هَٰذِهِ الشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ الظَّالِمِينَ(19) "Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai." |
فَوَسْوَسَ لَهُمَا الشَّيْطَانُ لِيُبْدِيَ لَهُمَا مَا وُورِيَ عَنْهُمَا مِن سَوْآتِهِمَا وَقَالَ مَا نَهَاكُمَا رَبُّكُمَا عَنْ هَٰذِهِ الشَّجَرَةِ إِلَّا أَن تَكُونَا مَلَكَيْنِ أَوْ تَكُونَا مِنَ الْخَالِدِينَ(20) Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama." |
وَقَاسَمَهُمَا إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ النَّاصِحِينَ(21) Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne. |
فَدَلَّاهُمَا بِغُرُورٍ ۚ فَلَمَّا ذَاقَا الشَّجَرَةَ بَدَتْ لَهُمَا سَوْآتُهُمَا وَطَفِقَا يَخْصِفَانِ عَلَيْهِمَا مِن وَرَقِ الْجَنَّةِ ۖ وَنَادَاهُمَا رَبُّهُمَا أَلَمْ أَنْهَكُمَا عَن تِلْكُمَا الشَّجَرَةِ وَأَقُل لَّكُمَا إِنَّ الشَّيْطَانَ لَكُمَا عَدُوٌّ مُّبِينٌ(22) Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?" |
قَالَا رَبَّنَا ظَلَمْنَا أَنفُسَنَا وَإِن لَّمْ تَغْفِرْ لَنَا وَتَرْحَمْنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ(23) Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra." |
قَالَ اهْبِطُوا بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ ۖ وَلَكُمْ فِي الْأَرْضِ مُسْتَقَرٌّ وَمَتَاعٌ إِلَىٰ حِينٍ(24) Ya ce: "Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi." |
قَالَ فِيهَا تَحْيَوْنَ وَفِيهَا تَمُوتُونَ وَمِنْهَا تُخْرَجُونَ(25) Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku." |
يَا بَنِي آدَمَ قَدْ أَنزَلْنَا عَلَيْكُمْ لِبَاسًا يُوَارِي سَوْآتِكُمْ وَرِيشًا ۖ وَلِبَاسُ التَّقْوَىٰ ذَٰلِكَ خَيْرٌ ۚ ذَٰلِكَ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ(26) Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa! |
يَا بَنِي آدَمَ لَا يَفْتِنَنَّكُمُ الشَّيْطَانُ كَمَا أَخْرَجَ أَبَوَيْكُم مِّنَ الْجَنَّةِ يَنزِعُ عَنْهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوْآتِهِمَا ۗ إِنَّهُ يَرَاكُمْ هُوَ وَقَبِيلُهُ مِنْ حَيْثُ لَا تَرَوْنَهُمْ ۗ إِنَّا جَعَلْنَا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ(27) Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni. |
وَإِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً قَالُوا وَجَدْنَا عَلَيْهَا آبَاءَنَا وَاللَّهُ أَمَرَنَا بِهَا ۗ قُلْ إِنَّ اللَّهَ لَا يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاءِ ۖ أَتَقُولُونَ عَلَى اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ(28) Kuma idan suka aikata alfãsha su ce: "Mun sãmi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?" |
قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ ۖ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ ۚ كَمَا بَدَأَكُمْ تَعُودُونَ(29) Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa." |
فَرِيقًا هَدَىٰ وَفَرِيقًا حَقَّ عَلَيْهِمُ الضَّلَالَةُ ۗ إِنَّهُمُ اتَّخَذُوا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ اللَّهِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُّهْتَدُونَ(30) Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne. |
۞ يَا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَكُلُوا وَاشْرَبُوا وَلَا تُسْرِفُوا ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُسْرِفِينَ(31) Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna. |
قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللَّهِ الَّتِي أَخْرَجَ لِعِبَادِهِ وَالطَّيِّبَاتِ مِنَ الرِّزْقِ ۚ قُلْ هِيَ لِلَّذِينَ آمَنُوا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا خَالِصَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ(32) Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani. |
قُلْ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَالْإِثْمَ وَالْبَغْيَ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَأَن تُشْرِكُوا بِاللَّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَأَن تَقُولُوا عَلَى اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ(33) Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah." |
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ ۖ فَإِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ لَا يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ(34) Kuma ga kõwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba. |
يَا بَنِي آدَمَ إِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي ۙ فَمَنِ اتَّقَىٰ وَأَصْلَحَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ(35) Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki. |
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُوا عَنْهَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ(36) Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne. |
فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ ۚ أُولَٰئِكَ يَنَالُهُمْ نَصِيبُهُم مِّنَ الْكِتَابِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَاءَتْهُمْ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوْنَهُمْ قَالُوا أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللَّهِ ۖ قَالُوا ضَلُّوا عَنَّا وَشَهِدُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ أَنَّهُمْ كَانُوا كَافِرِينَ(37) To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai." |
قَالَ ادْخُلُوا فِي أُمَمٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِكُم مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ فِي النَّارِ ۖ كُلَّمَا دَخَلَتْ أُمَّةٌ لَّعَنَتْ أُخْتَهَا ۖ حَتَّىٰ إِذَا ادَّارَكُوا فِيهَا جَمِيعًا قَالَتْ أُخْرَاهُمْ لِأُولَاهُمْ رَبَّنَا هَٰؤُلَاءِ أَضَلُّونَا فَآتِهِمْ عَذَابًا ضِعْفًا مِّنَ النَّارِ ۖ قَالَ لِكُلٍّ ضِعْفٌ وَلَٰكِن لَّا تَعْلَمُونَ(38) Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba." |
وَقَالَتْ أُولَاهُمْ لِأُخْرَاهُمْ فَمَا كَانَ لَكُمْ عَلَيْنَا مِن فَضْلٍ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ(39) Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa!" |
إِنَّ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُوا عَنْهَا لَا تُفَتَّحُ لَهُمْ أَبْوَابُ السَّمَاءِ وَلَا يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّىٰ يَلِجَ الْجَمَلُ فِي سَمِّ الْخِيَاطِ ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُجْرِمِينَ(40) Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi. |
لَهُم مِّن جَهَنَّمَ مِهَادٌ وَمِن فَوْقِهِمْ غَوَاشٍ ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ(41) Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai. |
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ(42) Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne. |
وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ ۖ وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي هَدَانَا لِهَٰذَا وَمَا كُنَّا لِنَهْتَدِيَ لَوْلَا أَنْ هَدَانَا اللَّهُ ۖ لَقَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ ۖ وَنُودُوا أَن تِلْكُمُ الْجَنَّةُ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ(43) Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa." |
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ أَصْحَابَ النَّارِ أَن قَدْ وَجَدْنَا مَا وَعَدَنَا رَبُّنَا حَقًّا فَهَلْ وَجَدتُّم مَّا وَعَدَ رَبُّكُمْ حَقًّا ۖ قَالُوا نَعَمْ ۚ فَأَذَّنَ مُؤَذِّنٌ بَيْنَهُمْ أَن لَّعْنَةُ اللَّهِ عَلَى الظَّالِمِينَ(44) Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai." |
الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللَّهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجًا وَهُم بِالْآخِرَةِ كَافِرُونَ(45) "Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne." |
وَبَيْنَهُمَا حِجَابٌ ۚ وَعَلَى الْأَعْرَافِ رِجَالٌ يَعْرِفُونَ كُلًّا بِسِيمَاهُمْ ۚ وَنَادَوْا أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَن سَلَامٌ عَلَيْكُمْ ۚ لَمْ يَدْخُلُوهَا وَهُمْ يَطْمَعُونَ(46) Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni. |
۞ وَإِذَا صُرِفَتْ أَبْصَارُهُمْ تِلْقَاءَ أَصْحَابِ النَّارِ قَالُوا رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ(47) Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai." |
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ الْأَعْرَافِ رِجَالًا يَعْرِفُونَهُم بِسِيمَاهُمْ قَالُوا مَا أَغْنَىٰ عَنكُمْ جَمْعُكُمْ وَمَا كُنتُمْ تَسْتَكْبِرُونَ(48) Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: "Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku?" |
أَهَٰؤُلَاءِ الَّذِينَ أَقْسَمْتُمْ لَا يَنَالُهُمُ اللَّهُ بِرَحْمَةٍ ۚ ادْخُلُوا الْجَنَّةَ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمْ وَلَا أَنتُمْ تَحْزَنُونَ(49) "Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro akanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba." |
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ النَّارِ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَنْ أَفِيضُوا عَلَيْنَا مِنَ الْمَاءِ أَوْ مِمَّا رَزَقَكُمُ اللَّهُ ۚ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ حَرَّمَهُمَا عَلَى الْكَافِرِينَ(50) Kuma 'yan wuta suka kirãyi 'yan Aljanna cẽwa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai." |
الَّذِينَ اتَّخَذُوا دِينَهُمْ لَهْوًا وَلَعِبًا وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا ۚ فَالْيَوْمَ نَنسَاهُمْ كَمَا نَسُوا لِقَاءَ يَوْمِهِمْ هَٰذَا وَمَا كَانُوا بِآيَاتِنَا يَجْحَدُونَ(51) "Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu. |
وَلَقَدْ جِئْنَاهُم بِكِتَابٍ فَصَّلْنَاهُ عَلَىٰ عِلْمٍ هُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ(52) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani. |
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا تَأْوِيلَهُ ۚ يَوْمَ يَأْتِي تَأْوِيلُهُ يَقُولُ الَّذِينَ نَسُوهُ مِن قَبْلُ قَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ فَهَل لَّنَا مِن شُفَعَاءَ فَيَشْفَعُوا لَنَا أَوْ نُرَدُّ فَنَعْمَلَ غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ ۚ قَدْ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ(53) Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?" Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu. |
إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ ۗ أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ ۗ تَبَارَكَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ(54) Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana! |
ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْيَةً ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ(55) Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsuwuce iyãka. |
وَلَا تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ بَعْدَ إِصْلَاحِهَا وَادْعُوهُ خَوْفًا وَطَمَعًا ۚ إِنَّ رَحْمَتَ اللَّهِ قَرِيبٌ مِّنَ الْمُحْسِنِينَ(56) Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa. |
وَهُوَ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا أَقَلَّتْ سَحَابًا ثِقَالًا سُقْنَاهُ لِبَلَدٍ مَّيِّتٍ فَأَنزَلْنَا بِهِ الْمَاءَ فَأَخْرَجْنَا بِهِ مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ ۚ كَذَٰلِكَ نُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ(57) Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi, sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni. |
وَالْبَلَدُ الطَّيِّبُ يَخْرُجُ نَبَاتُهُ بِإِذْنِ رَبِّهِ ۖ وَالَّذِي خَبُثَ لَا يَخْرُجُ إِلَّا نَكِدًا ۚ كَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَشْكُرُونَ(58) Kuma gari mai kyau, tsirinsa yanã fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bã ya fita, fãce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ãyõyi dõmin mutãne waɗanda suke gõdẽwa. |
لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ(59) Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku tsõron azãbar wani Yini mai girma." |
قَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ(60) Mashawarta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya." |
قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي ضَلَالَةٌ وَلَٰكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ(61) Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu!" |
أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنصَحُ لَكُمْ وَأَعْلَمُ مِنَ اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ(62) "Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba. |
أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءَكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ وَلِتَتَّقُوا وَلَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ(63) "Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku?" |
فَكَذَّبُوهُ فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ فِي الْفُلْكِ وَأَغْرَقْنَا الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا عَمِينَ(64) Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu. |
۞ وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ(65) Kuma zuwa ga Ãdãwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?" |
قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي سَفَاهَةٍ وَإِنَّا لَنَظُنُّكَ مِنَ الْكَاذِبِينَ(66) Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata." |
قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي سَفَاهَةٌ وَلَٰكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ(67) Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!" |
أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنَا لَكُمْ نَاصِحٌ أَمِينٌ(68) Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce. |
أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءَكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ ۚ وَاذْكُرُوا إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاءَ مِن بَعْدِ قَوْمِ نُوحٍ وَزَادَكُمْ فِي الْخَلْقِ بَسْطَةً ۖ فَاذْكُرُوا آلَاءَ اللَّهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ(69) "Shin, kuma kun yi mãmãki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya sanyã ku mãsu mayẽwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin halitta. Sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara." |
قَالُوا أَجِئْتَنَا لِنَعْبُدَ اللَّهَ وَحْدَهُ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا ۖ فَأْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ(70) Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya." |
قَالَ قَدْ وَقَعَ عَلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ رِجْسٌ وَغَضَبٌ ۖ أَتُجَادِلُونَنِي فِي أَسْمَاءٍ سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا نَزَّلَ اللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ فَانتَظِرُوا إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ(71) Ya ce: "Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tãre da ku mai jira ne." |
فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَقَطَعْنَا دَابِرَ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۖ وَمَا كَانُوا مُؤْمِنِينَ(72) To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba. |
وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ قَدْ جَاءَتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ ۖ هَٰذِهِ نَاقَةُ اللَّهِ لَكُمْ آيَةً ۖ فَذَرُوهَا تَأْكُلْ فِي أَرْضِ اللَّهِ ۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ(73) Kuma zuwa ga Samũdãwa ɗan'uwansu, Sãlihu, ya ce: "Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku." |
وَاذْكُرُوا إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاءَ مِن بَعْدِ عَادٍ وَبَوَّأَكُمْ فِي الْأَرْضِ تَتَّخِذُونَ مِن سُهُولِهَا قُصُورًا وَتَنْحِتُونَ الْجِبَالَ بُيُوتًا ۖ فَاذْكُرُوا آلَاءَ اللَّهِ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ(74) "Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi." |
قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا مِن قَوْمِهِ لِلَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِمَنْ آمَنَ مِنْهُمْ أَتَعْلَمُونَ أَنَّ صَالِحًا مُّرْسَلٌ مِّن رَّبِّهِ ۚ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلَ بِهِ مُؤْمِنُونَ(75) Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar, ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: "Shin, kunã sanin cẽwaSãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu ĩmãni ne." |
قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا إِنَّا بِالَّذِي آمَنتُم بِهِ كَافِرُونَ(76) Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne." |
فَعَقَرُوا النَّاقَةَ وَعَتَوْا عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ وَقَالُوا يَا صَالِحُ ائْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الْمُرْسَلِينَ(77) Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kã kasance daga manzanni!" |
فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ(78) Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne! |
فَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُحِبُّونَ النَّاصِحِينَ(79) Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha!" |
وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِّنَ الْعَالَمِينَ(80) Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: "Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?" |
إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَةً مِّن دُونِ النِّسَاءِ ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ مُّسْرِفُونَ(81) "Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata." |
وَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا أَخْرِجُوهُم مِّن قَرْيَتِكُمْ ۖ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ(82) Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da'awar tsarki!" |
فَأَنجَيْنَاهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ(83) Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa. |
وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِينَ(84) Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance! |
وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ قَدْ جَاءَتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ ۖ فَأَوْفُوا الْكَيْلَ وَالْمِيزَانَ وَلَا تَبْخَسُوا النَّاسَ أَشْيَاءَهُمْ وَلَا تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ بَعْدَ إِصْلَاحِهَا ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ(85) Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai." |
وَلَا تَقْعُدُوا بِكُلِّ صِرَاطٍ تُوعِدُونَ وَتَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللَّهِ مَنْ آمَنَ بِهِ وَتَبْغُونَهَا عِوَجًا ۚ وَاذْكُرُوا إِذْ كُنتُمْ قَلِيلًا فَكَثَّرَكُمْ ۖ وَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ(86) "Kuma kada ku zauna ga kõwane tafarki kunã ƙyacẽwa, kuma kunã kangẽwa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma kunã nẽman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lõkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu fasãdi ta kasance:" |
وَإِن كَانَ طَائِفَةٌ مِّنكُمْ آمَنُوا بِالَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ وَطَائِفَةٌ لَّمْ يُؤْمِنُوا فَاصْبِرُوا حَتَّىٰ يَحْكُمَ اللَّهُ بَيْنَنَا ۚ وَهُوَ خَيْرُ الْحَاكِمِينَ(87) "Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmãni da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmãni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakãninmu; kuma Shi ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci." |
۞ قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا مِن قَوْمِهِ لَنُخْرِجَنَّكَ يَا شُعَيْبُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَكَ مِن قَرْيَتِنَا أَوْ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَا ۚ قَالَ أَوَلَوْ كُنَّا كَارِهِينَ(88) Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?" |
قَدِ افْتَرَيْنَا عَلَى اللَّهِ كَذِبًا إِنْ عُدْنَا فِي مِلَّتِكُم بَعْدَ إِذْ نَجَّانَا اللَّهُ مِنْهَا ۚ وَمَا يَكُونُ لَنَا أَن نَّعُودَ فِيهَا إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّنَا ۚ وَسِعَ رَبُّنَا كُلَّ شَيْءٍ عِلْمًا ۚ عَلَى اللَّهِ تَوَكَّلْنَا ۚ رَبَّنَا افْتَحْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ قَوْمِنَا بِالْحَقِّ وَأَنتَ خَيْرُ الْفَاتِحِينَ(89) "Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci." |
وَقَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ لَئِنِ اتَّبَعْتُمْ شُعَيْبًا إِنَّكُمْ إِذًا لَّخَاسِرُونَ(90) Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne." |
فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ(91) Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne. |
الَّذِينَ كَذَّبُوا شُعَيْبًا كَأَن لَّمْ يَغْنَوْا فِيهَا ۚ الَّذِينَ كَذَّبُوا شُعَيْبًا كَانُوا هُمُ الْخَاسِرِينَ(92) Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra! |
فَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ ۖ فَكَيْفَ آسَىٰ عَلَىٰ قَوْمٍ كَافِرِينَ(93) Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?" |
وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا أَخَذْنَا أَهْلَهَا بِالْبَأْسَاءِ وَالضَّرَّاءِ لَعَلَّهُمْ يَضَّرَّعُونَ(94) Kuma ba Mu aika wani Annabi a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai. |
ثُمَّ بَدَّلْنَا مَكَانَ السَّيِّئَةِ الْحَسَنَةَ حَتَّىٰ عَفَوا وَّقَالُوا قَدْ مَسَّ آبَاءَنَا الضَّرَّاءُ وَالسَّرَّاءُ فَأَخَذْنَاهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ(95) Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." (sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa." |
وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَىٰ آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِم بَرَكَاتٍ مِّنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ وَلَٰكِن كَذَّبُوا فَأَخَذْنَاهُم بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ(96) Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa. |
أَفَأَمِنَ أَهْلُ الْقُرَىٰ أَن يَأْتِيَهُم بَأْسُنَا بَيَاتًا وَهُمْ نَائِمُونَ(97) Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci? |
أَوَأَمِنَ أَهْلُ الْقُرَىٰ أَن يَأْتِيَهُم بَأْسُنَا ضُحًى وَهُمْ يَلْعَبُونَ(98) Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa? |
أَفَأَمِنُوا مَكْرَ اللَّهِ ۚ فَلَا يَأْمَنُ مَكْرَ اللَّهِ إِلَّا الْقَوْمُ الْخَاسِرُونَ(99) Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra! |
أَوَلَمْ يَهْدِ لِلَّذِينَ يَرِثُونَ الْأَرْضَ مِن بَعْدِ أَهْلِهَا أَن لَّوْ نَشَاءُ أَصَبْنَاهُم بِذُنُوبِهِمْ ۚ وَنَطْبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَسْمَعُونَ(100) Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji? |
تِلْكَ الْقُرَىٰ نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنبَائِهَا ۚ وَلَقَدْ جَاءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا كَانُوا لِيُؤْمِنُوا بِمَا كَذَّبُوا مِن قَبْلُ ۚ كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ اللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ الْكَافِرِينَ(101) Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukãtan kãfirai. |
وَمَا وَجَدْنَا لِأَكْثَرِهِم مِّنْ عَهْدٍ ۖ وَإِن وَجَدْنَا أَكْثَرَهُمْ لَفَاسِقِينَ(102) Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai. |
ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِم مُّوسَىٰ بِآيَاتِنَا إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَظَلَمُوا بِهَا ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ(103) Sa'an nan kuma Mun aika Musa, daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take. |
وَقَالَ مُوسَىٰ يَا فِرْعَوْنُ إِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ(104) Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu." |
حَقِيقٌ عَلَىٰ أَن لَّا أَقُولَ عَلَى اللَّهِ إِلَّا الْحَقَّ ۚ قَدْ جِئْتُكُم بِبَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَرْسِلْ مَعِيَ بَنِي إِسْرَائِيلَ(105) "Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni." |
قَالَ إِن كُنتَ جِئْتَ بِآيَةٍ فَأْتِ بِهَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ(106) Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya." |
فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ(107) Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne! |
وَنَزَعَ يَدَهُ فَإِذَا هِيَ بَيْضَاءُ لِلنَّاظِرِينَ(108) Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi! |
قَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ إِنَّ هَٰذَا لَسَاحِرٌ عَلِيمٌ(109) Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi." |
يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُمْ ۖ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ(110) " Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?" |
قَالُوا أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَأَرْسِلْ فِي الْمَدَائِنِ حَاشِرِينَ(111) Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa. |
يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ(112) "Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi." |
وَجَاءَ السَّحَرَةُ فِرْعَوْنَ قَالُوا إِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ الْغَالِبِينَ(113) Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?" |
قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ لَمِنَ الْمُقَرَّبِينَ(114) Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta." |
قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِمَّا أَن تُلْقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ نَحْنُ الْمُلْقِينَ(115) Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?" |
قَالَ أَلْقُوا ۖ فَلَمَّا أَلْقَوْا سَحَرُوا أَعْيُنَ النَّاسِ وَاسْتَرْهَبُوهُمْ وَجَاءُوا بِسِحْرٍ عَظِيمٍ(116) Ya ce: "Ku jẽfa." To a 1õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma." |
۞ وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ(117) Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi! |
فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ(118) Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci. |
فَغُلِبُوا هُنَالِكَ وَانقَلَبُوا صَاغِرِينَ(119) Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu. |
وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ(120) Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada. |
قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ الْعَالَمِينَ(121) Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu." |
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَارُونَ(122) "Ubangijin Mũsã da Harũna." |
قَالَ فِرْعَوْنُ آمَنتُم بِهِ قَبْلَ أَنْ آذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّ هَٰذَا لَمَكْرٌ مَّكَرْتُمُوهُ فِي الْمَدِينَةِ لِتُخْرِجُوا مِنْهَا أَهْلَهَا ۖ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ(123) Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani." |
لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَافٍ ثُمَّ لَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ(124) "Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya." |
قَالُوا إِنَّا إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ(125) Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne." |
وَمَا تَنقِمُ مِنَّا إِلَّا أَنْ آمَنَّا بِآيَاتِ رَبِّنَا لَمَّا جَاءَتْنَا ۚ رَبَّنَا أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْرًا وَتَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ(126) "Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! " |
وَقَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ أَتَذَرُ مُوسَىٰ وَقَوْمَهُ لِيُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ وَيَذَرَكَ وَآلِهَتَكَ ۚ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبْنَاءَهُمْ وَنَسْتَحْيِي نِسَاءَهُمْ وَإِنَّا فَوْقَهُمْ قَاهِرُونَ(127) Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne." |
قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ اسْتَعِينُوا بِاللَّهِ وَاصْبِرُوا ۖ إِنَّ الْأَرْضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ ۖ وَالْعَاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ(128) Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce." |
قَالُوا أُوذِينَا مِن قَبْلِ أَن تَأْتِيَنَا وَمِن بَعْدِ مَا جِئْتَنَا ۚ قَالَ عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُهْلِكَ عَدُوَّكُمْ وَيَسْتَخْلِفَكُمْ فِي الْأَرْضِ فَيَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ(129) Suka ce: "An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa." |
وَلَقَدْ أَخَذْنَا آلَ فِرْعَوْنَ بِالسِّنِينَ وَنَقْصٍ مِّنَ الثَّمَرَاتِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ(130) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa. |
فَإِذَا جَاءَتْهُمُ الْحَسَنَةُ قَالُوا لَنَا هَٰذِهِ ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ يَطَّيَّرُوا بِمُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُ ۗ أَلَا إِنَّمَا طَائِرُهُمْ عِندَ اللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ(131) Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: "Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani!" |
وَقَالُوا مَهْمَا تَأْتِنَا بِهِ مِنْ آيَةٍ لِّتَسْحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحْنُ لَكَ بِمُؤْمِنِينَ(132) Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba." |
فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ الطُّوفَانَ وَالْجَرَادَ وَالْقُمَّلَ وَالضَّفَادِعَ وَالدَّمَ آيَاتٍ مُّفَصَّلَاتٍ فَاسْتَكْبَرُوا وَكَانُوا قَوْمًا مُّجْرِمِينَ(133) Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi. |
وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيْهِمُ الرِّجْزُ قَالُوا يَا مُوسَى ادْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ ۖ لَئِن كَشَفْتَ عَنَّا الرِّجْزَ لَنُؤْمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرْسِلَنَّ مَعَكَ بَنِي إِسْرَائِيلَ(134) Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai." |
فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ الرِّجْزَ إِلَىٰ أَجَلٍ هُم بَالِغُوهُ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَ(135) To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa! |
فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا عَنْهَا غَافِلِينَ(136) Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai. |
وَأَوْرَثْنَا الْقَوْمَ الَّذِينَ كَانُوا يُسْتَضْعَفُونَ مَشَارِقَ الْأَرْضِ وَمَغَارِبَهَا الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا ۖ وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ الْحُسْنَىٰ عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ بِمَا صَبَرُوا ۖ وَدَمَّرْنَا مَا كَانَ يَصْنَعُ فِرْعَوْنُ وَقَوْمُهُ وَمَا كَانُوا يَعْرِشُونَ(137) Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa. |
وَجَاوَزْنَا بِبَنِي إِسْرَائِيلَ الْبَحْرَ فَأَتَوْا عَلَىٰ قَوْمٍ يَعْكُفُونَ عَلَىٰ أَصْنَامٍ لَّهُمْ ۚ قَالُوا يَا مُوسَى اجْعَل لَّنَا إِلَٰهًا كَمَا لَهُمْ آلِهَةٌ ۚ قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ(138) Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa " Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta." |
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ مُتَبَّرٌ مَّا هُمْ فِيهِ وَبَاطِلٌ مَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ(139) "Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne." |
قَالَ أَغَيْرَ اللَّهِ أَبْغِيكُمْ إِلَٰهًا وَهُوَ فَضَّلَكُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ(140) Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?" |
وَإِذْ أَنجَيْنَاكُم مِّنْ آلِ فِرْعَوْنَ يَسُومُونَكُمْ سُوءَ الْعَذَابِ ۖ يُقَتِّلُونَ أَبْنَاءَكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَاءَكُمْ ۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَاءٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَظِيمٌ(141) Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku, Mai girma. |
۞ وَوَاعَدْنَا مُوسَىٰ ثَلَاثِينَ لَيْلَةً وَأَتْمَمْنَاهَا بِعَشْرٍ فَتَمَّ مِيقَاتُ رَبِّهِ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَارُونَ اخْلُفْنِي فِي قَوْمِي وَأَصْلِحْ وَلَا تَتَّبِعْ سَبِيلَ الْمُفْسِدِينَ(142) Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi." |
وَلَمَّا جَاءَ مُوسَىٰ لِمِيقَاتِنَا وَكَلَّمَهُ رَبُّهُ قَالَ رَبِّ أَرِنِي أَنظُرْ إِلَيْكَ ۚ قَالَ لَن تَرَانِي وَلَٰكِنِ انظُرْ إِلَى الْجَبَلِ فَإِنِ اسْتَقَرَّ مَكَانَهُ فَسَوْفَ تَرَانِي ۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُ لِلْجَبَلِ جَعَلَهُ دَكًّا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقًا ۚ فَلَمَّا أَفَاقَ قَالَ سُبْحَانَكَ تُبْتُ إِلَيْكَ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُؤْمِنِينَ(143) Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai." |
قَالَ يَا مُوسَىٰ إِنِّي اصْطَفَيْتُكَ عَلَى النَّاسِ بِرِسَالَاتِي وَبِكَلَامِي فَخُذْ مَا آتَيْتُكَ وَكُن مِّنَ الشَّاكِرِينَ(144) Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya." |
وَكَتَبْنَا لَهُ فِي الْأَلْوَاحِ مِن كُلِّ شَيْءٍ مَّوْعِظَةً وَتَفْصِيلًا لِّكُلِّ شَيْءٍ فَخُذْهَا بِقُوَّةٍ وَأْمُرْ قَوْمَكَ يَأْخُذُوا بِأَحْسَنِهَا ۚ سَأُرِيكُمْ دَارَ الْفَاسِقِينَ(145) Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai." |
سَأَصْرِفُ عَنْ آيَاتِيَ الَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَإِن يَرَوْا كُلَّ آيَةٍ لَّا يُؤْمِنُوا بِهَا وَإِن يَرَوْا سَبِيلَ الرُّشْدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا وَإِن يَرَوْا سَبِيلَ الْغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا عَنْهَا غَافِلِينَ(146) Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai. |
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَلِقَاءِ الْآخِرَةِ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ ۚ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ(147) Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa? |
وَاتَّخَذَ قَوْمُ مُوسَىٰ مِن بَعْدِهِ مِنْ حُلِيِّهِمْ عِجْلًا جَسَدًا لَّهُ خُوَارٌ ۚ أَلَمْ يَرَوْا أَنَّهُ لَا يُكَلِّمُهُمْ وَلَا يَهْدِيهِمْ سَبِيلًا ۘ اتَّخَذُوهُ وَكَانُوا ظَالِمِينَ(148) Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci. |
وَلَمَّا سُقِطَ فِي أَيْدِيهِمْ وَرَأَوْا أَنَّهُمْ قَدْ ضَلُّوا قَالُوا لَئِن لَّمْ يَرْحَمْنَا رَبُّنَا وَيَغْفِرْ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ(149) Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra." |
وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰ إِلَىٰ قَوْمِهِ غَضْبَانَ أَسِفًا قَالَ بِئْسَمَا خَلَفْتُمُونِي مِن بَعْدِي ۖ أَعَجِلْتُمْ أَمْرَ رَبِّكُمْ ۖ وَأَلْقَى الْأَلْوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأْسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُ إِلَيْهِ ۚ قَالَ ابْنَ أُمَّ إِنَّ الْقَوْمَ اسْتَضْعَفُونِي وَكَادُوا يَقْتُلُونَنِي فَلَا تُشْمِتْ بِيَ الْأَعْدَاءَ وَلَا تَجْعَلْنِي مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ(150) Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã ɗan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne azzãlumai." |
قَالَ رَبِّ اغْفِرْ لِي وَلِأَخِي وَأَدْخِلْنَا فِي رَحْمَتِكَ ۖ وَأَنتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ(151) Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!" |
إِنَّ الَّذِينَ اتَّخَذُوا الْعِجْلَ سَيَنَالُهُمْ غَضَبٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَذِلَّةٌ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُفْتَرِينَ(152) Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya. |
وَالَّذِينَ عَمِلُوا السَّيِّئَاتِ ثُمَّ تَابُوا مِن بَعْدِهَا وَآمَنُوا إِنَّ رَبَّكَ مِن بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ(153) Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma sukayi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfarane, Mai jin ƙai. |
وَلَمَّا سَكَتَ عَن مُّوسَى الْغَضَبُ أَخَذَ الْأَلْوَاحَ ۖ وَفِي نُسْخَتِهَا هُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلَّذِينَ هُمْ لِرَبِّهِمْ يَرْهَبُونَ(154) Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne. |
وَاخْتَارَ مُوسَىٰ قَوْمَهُ سَبْعِينَ رَجُلًا لِّمِيقَاتِنَا ۖ فَلَمَّا أَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ قَالَ رَبِّ لَوْ شِئْتَ أَهْلَكْتَهُم مِّن قَبْلُ وَإِيَّايَ ۖ أَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ السُّفَهَاءُ مِنَّا ۖ إِنْ هِيَ إِلَّا فِتْنَتُكَ تُضِلُّ بِهَا مَن تَشَاءُ وَتَهْدِي مَن تَشَاءُ ۖ أَنتَ وَلِيُّنَا فَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا ۖ وَأَنتَ خَيْرُ الْغَافِرِينَ(155) Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba'in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara." |
۞ وَاكْتُبْ لَنَا فِي هَٰذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الْآخِرَةِ إِنَّا هُدْنَا إِلَيْكَ ۚ قَالَ عَذَابِي أُصِيبُ بِهِ مَنْ أَشَاءُ ۖ وَرَحْمَتِي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ ۚ فَسَأَكْتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَالَّذِينَ هُم بِآيَاتِنَا يُؤْمِنُونَ(156) "Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu mũminai ne." |
الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ الرَّسُولَ النَّبِيَّ الْأُمِّيَّ الَّذِي يَجِدُونَهُ مَكْتُوبًا عِندَهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنجِيلِ يَأْمُرُهُم بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَاهُمْ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ الطَّيِّبَاتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيْهِمُ الْخَبَائِثَ وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَالْأَغْلَالَ الَّتِي كَانَتْ عَلَيْهِمْ ۚ فَالَّذِينَ آمَنُوا بِهِ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَاتَّبَعُوا النُّورَ الَّذِي أُنزِلَ مَعَهُ ۙ أُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ(157) "Waɗanda suke sunã bin Manzo, Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla. |
قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ فَآمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الْأُمِّيِّ الَّذِي يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَكَلِمَاتِهِ وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ(158) Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa." |
وَمِن قَوْمِ مُوسَىٰ أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَبِهِ يَعْدِلُونَ(159) Kuma daga mutãnen Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci. |
وَقَطَّعْنَاهُمُ اثْنَتَيْ عَشْرَةَ أَسْبَاطًا أُمَمًا ۚ وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ إِذِ اسْتَسْقَاهُ قَوْمُهُ أَنِ اضْرِب بِّعَصَاكَ الْحَجَرَ ۖ فَانبَجَسَتْ مِنْهُ اثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْنًا ۖ قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍ مَّشْرَبَهُمْ ۚ وَظَلَّلْنَا عَلَيْهِمُ الْغَمَامَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْهِمُ الْمَنَّ وَالسَّلْوَىٰ ۖ كُلُوا مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ ۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ(160) Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta. |
وَإِذْ قِيلَ لَهُمُ اسْكُنُوا هَٰذِهِ الْقَرْيَةَ وَكُلُوا مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ وَقُولُوا حِطَّةٌ وَادْخُلُوا الْبَابَ سُجَّدًا نَّغْفِرْ لَكُمْ خَطِيئَاتِكُمْ ۚ سَنَزِيدُ الْمُحْسِنِينَ(161) Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya, kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa." |
فَبَدَّلَ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْهُمْ قَوْلًا غَيْرَ الَّذِي قِيلَ لَهُمْ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِجْزًا مِّنَ السَّمَاءِ بِمَا كَانُوا يَظْلِمُونَ(162) Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci. |
وَاسْأَلْهُمْ عَنِ الْقَرْيَةِ الَّتِي كَانَتْ حَاضِرَةَ الْبَحْرِ إِذْ يَعْدُونَ فِي السَّبْتِ إِذْ تَأْتِيهِمْ حِيتَانُهُمْ يَوْمَ سَبْتِهِمْ شُرَّعًا وَيَوْمَ لَا يَسْبِتُونَ ۙ لَا تَأْتِيهِمْ ۚ كَذَٰلِكَ نَبْلُوهُم بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ(163) Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci. |
وَإِذْ قَالَتْ أُمَّةٌ مِّنْهُمْ لِمَ تَعِظُونَ قَوْمًا ۙ اللَّهُ مُهْلِكُهُمْ أَوْ مُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا شَدِيدًا ۖ قَالُوا مَعْذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ(164) Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa." |
فَلَمَّا نَسُوا مَا ذُكِّرُوا بِهِ أَنجَيْنَا الَّذِينَ يَنْهَوْنَ عَنِ السُّوءِ وَأَخَذْنَا الَّذِينَ ظَلَمُوا بِعَذَابٍ بَئِيسٍ بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ(165) To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci. |
فَلَمَّا عَتَوْا عَن مَّا نُهُوا عَنْهُ قُلْنَا لَهُمْ كُونُوا قِرَدَةً خَاسِئِينَ(166) Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu." |
وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكَ لَيَبْعَثَنَّ عَلَيْهِمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَن يَسُومُهُمْ سُوءَ الْعَذَابِ ۗ إِنَّ رَبَّكَ لَسَرِيعُ الْعِقَابِ ۖ وَإِنَّهُ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ(167) Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar¡iyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
وَقَطَّعْنَاهُمْ فِي الْأَرْضِ أُمَمًا ۖ مِّنْهُمُ الصَّالِحُونَ وَمِنْهُمْ دُونَ ذَٰلِكَ ۖ وَبَلَوْنَاهُم بِالْحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ(168) Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa. |
فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ وَرِثُوا الْكِتَابَ يَأْخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا الْأَدْنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغْفَرُ لَنَا وَإِن يَأْتِهِمْ عَرَضٌ مِّثْلُهُ يَأْخُذُوهُ ۚ أَلَمْ يُؤْخَذْ عَلَيْهِم مِّيثَاقُ الْكِتَابِ أَن لَّا يَقُولُوا عَلَى اللَّهِ إِلَّا الْحَقَّ وَدَرَسُوا مَا فِيهِ ۗ وَالدَّارُ الْآخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ(169) Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba? |
وَالَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِالْكِتَابِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ الْمُصْلِحِينَ(170) Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa. |
۞ وَإِذْ نَتَقْنَا الْجَبَلَ فَوْقَهُمْ كَأَنَّهُ ظُلَّةٌ وَظَنُّوا أَنَّهُ وَاقِعٌ بِهِمْ خُذُوا مَا آتَيْنَاكُم بِقُوَّةٍ وَاذْكُرُوا مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ(171) Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa." |
وَإِذْ أَخَذَ رَبُّكَ مِن بَنِي آدَمَ مِن ظُهُورِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَأَشْهَدَهُمْ عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ أَلَسْتُ بِرَبِّكُمْ ۖ قَالُوا بَلَىٰ ۛ شَهِدْنَا ۛ أَن تَقُولُوا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّا كُنَّا عَنْ هَٰذَا غَافِلِينَ(172) Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne." |
أَوْ تَقُولُوا إِنَّمَا أَشْرَكَ آبَاؤُنَا مِن قَبْلُ وَكُنَّا ذُرِّيَّةً مِّن بَعْدِهِمْ ۖ أَفَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ الْمُبْطِلُونَ(173) Kõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa, Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata?" |
وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ وَلَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ(174) Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa. |
وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ الَّذِي آتَيْنَاهُ آيَاتِنَا فَانسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ الشَّيْطَانُ فَكَانَ مِنَ الْغَاوِينَ(175) Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku. |
وَلَوْ شِئْنَا لَرَفَعْنَاهُ بِهَا وَلَٰكِنَّهُ أَخْلَدَ إِلَى الْأَرْضِ وَاتَّبَعَ هَوَاهُ ۚ فَمَثَلُهُ كَمَثَلِ الْكَلْبِ إِن تَحْمِلْ عَلَيْهِ يَلْهَثْ أَوْ تَتْرُكْهُ يَلْهَث ۚ ذَّٰلِكَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ فَاقْصُصِ الْقَصَصَ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ(176) Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni. |
سَاءَ مَثَلًا الْقَوْمُ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَأَنفُسَهُمْ كَانُوا يَظْلِمُونَ(177) Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta. |
مَن يَهْدِ اللَّهُ فَهُوَ الْمُهْتَدِي ۖ وَمَن يُضْلِلْ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ(178) Wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. |
وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ بِهَا ۚ أُولَٰئِكَ كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ(179) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu. |
وَلِلَّهِ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَىٰ فَادْعُوهُ بِهَا ۖ وَذَرُوا الَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِي أَسْمَائِهِ ۚ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ(180) Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
وَمِمَّنْ خَلَقْنَا أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَبِهِ يَعْدِلُونَ(181) Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci. |
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لَا يَعْلَمُونَ(182) Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba. |
وَأُمْلِي لَهُمْ ۚ إِنَّ كَيْدِي مَتِينٌ(183) Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne. |
أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا ۗ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ(184) Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu? shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa. |
أَوَلَمْ يَنظُرُوا فِي مَلَكُوتِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا خَلَقَ اللَّهُ مِن شَيْءٍ وَأَنْ عَسَىٰ أَن يَكُونَ قَدِ اقْتَرَبَ أَجَلُهُمْ ۖ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ(185) Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni? |
مَن يُضْلِلِ اللَّهُ فَلَا هَادِيَ لَهُ ۚ وَيَذَرُهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ(186) Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa. |
يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ رَبِّي ۖ لَا يُجَلِّيهَا لِوَقْتِهَا إِلَّا هُوَ ۚ ثَقُلَتْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ لَا تَأْتِيكُمْ إِلَّا بَغْتَةً ۗ يَسْأَلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِيٌّ عَنْهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ اللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ(187) Sunã tambayar ka daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani." |
قُل لَّا أَمْلِكُ لِنَفْسِي نَفْعًا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ ۚ وَلَوْ كُنتُ أَعْلَمُ الْغَيْبَ لَاسْتَكْثَرْتُ مِنَ الْخَيْرِ وَمَا مَسَّنِيَ السُّوءُ ۚ إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ(188) Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni." |
۞ هُوَ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا لِيَسْكُنَ إِلَيْهَا ۖ فَلَمَّا تَغَشَّاهَا حَمَلَتْ حَمْلًا خَفِيفًا فَمَرَّتْ بِهِ ۖ فَلَمَّا أَثْقَلَت دَّعَوَا اللَّهَ رَبَّهُمَا لَئِنْ آتَيْتَنَا صَالِحًا لَّنَكُونَنَّ مِنَ الشَّاكِرِينَ(189) Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya." |
فَلَمَّا آتَاهُمَا صَالِحًا جَعَلَا لَهُ شُرَكَاءَ فِيمَا آتَاهُمَا ۚ فَتَعَالَى اللَّهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ(190) To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki. |
أَيُشْرِكُونَ مَا لَا يَخْلُقُ شَيْئًا وَهُمْ يُخْلَقُونَ(191) Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa? |
وَلَا يَسْتَطِيعُونَ لَهُمْ نَصْرًا وَلَا أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ(192) Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka! |
وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى الْهُدَىٰ لَا يَتَّبِعُوكُمْ ۚ سَوَاءٌ عَلَيْكُمْ أَدَعَوْتُمُوهُمْ أَمْ أَنتُمْ صَامِتُونَ(193) Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne! |
إِنَّ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللَّهِ عِبَادٌ أَمْثَالُكُمْ ۖ فَادْعُوهُمْ فَلْيَسْتَجِيبُوا لَكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ(194) Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya! |
أَلَهُمْ أَرْجُلٌ يَمْشُونَ بِهَا ۖ أَمْ لَهُمْ أَيْدٍ يَبْطِشُونَ بِهَا ۖ أَمْ لَهُمْ أَعْيُنٌ يُبْصِرُونَ بِهَا ۖ أَمْ لَهُمْ آذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا ۗ قُلِ ادْعُوا شُرَكَاءَكُمْ ثُمَّ كِيدُونِ فَلَا تُنظِرُونِ(195) Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini." |
إِنَّ وَلِيِّيَ اللَّهُ الَّذِي نَزَّلَ الْكِتَابَ ۖ وَهُوَ يَتَوَلَّى الصَّالِحِينَ(196) "Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai," |
وَالَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِهِ لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَكُمْ وَلَا أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ(197) "Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka." |
وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى الْهُدَىٰ لَا يَسْمَعُوا ۖ وَتَرَاهُمْ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ وَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ(198) Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani. |
خُذِ الْعَفْوَ وَأْمُرْ بِالْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ الْجَاهِلِينَ(199) Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai. |
وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ ۚ إِنَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ(200) Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani. |
إِنَّ الَّذِينَ اتَّقَوْا إِذَا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِّنَ الشَّيْطَانِ تَذَكَّرُوا فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ(201) Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra. |
وَإِخْوَانُهُمْ يَمُدُّونَهُمْ فِي الْغَيِّ ثُمَّ لَا يُقْصِرُونَ(202) Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa. |
وَإِذَا لَمْ تَأْتِهِم بِآيَةٍ قَالُوا لَوْلَا اجْتَبَيْتَهَا ۚ قُلْ إِنَّمَا أَتَّبِعُ مَا يُوحَىٰ إِلَيَّ مِن رَّبِّي ۚ هَٰذَا بَصَائِرُ مِن رَّبِّكُمْ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ(203) Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni." |
وَإِذَا قُرِئَ الْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ(204) Kuma idan an karanta Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama. |
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ(205) Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu. |
إِنَّ الَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لَا يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِهِ وَيُسَبِّحُونَهُ وَلَهُ يَسْجُدُونَ ۩(206) Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada. |