وَالصَّافَّاتِ صَفًّا(1) Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). |
فَالزَّاجِرَاتِ زَجْرًا(2) Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi. |
فَالتَّالِيَاتِ ذِكْرًا(3) Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. |
إِنَّ إِلَٰهَكُمْ لَوَاحِدٌ(4) Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. |
رَّبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ الْمَشَارِقِ(5) Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. |
إِنَّا زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِزِينَةٍ الْكَوَاكِبِ(6) Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. |
وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَانٍ مَّارِدٍ(7) Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. |
لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى الْمَلَإِ الْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ(8) Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. |
دُحُورًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌ(9) Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. |
إِلَّا مَنْ خَطِفَ الْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ ثَاقِبٌ(10) Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. |
فَاسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَا ۚ إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍ(11) Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri. |
بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَ(12) Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili. |
وَإِذَا ذُكِّرُوا لَا يَذْكُرُونَ(13) Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa. |
وَإِذَا رَأَوْا آيَةً يَسْتَسْخِرُونَ(14) Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili. |
وَقَالُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ(15) Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne." |
أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ(16) "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? |
أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ(17) "Ashe kõ da ubanninmu na farko?" |
قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَاخِرُونَ(18) Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." |
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَ(19) Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. |
وَقَالُوا يَا وَيْلَنَا هَٰذَا يَوْمُ الدِّينِ(20) Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." |
هَٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ(21) Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. |
۞ احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأَزْوَاجَهُمْ وَمَا كَانُوا يَعْبُدُونَ(22) Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. |
مِن دُونِ اللَّهِ فَاهْدُوهُمْ إِلَىٰ صِرَاطِ الْجَحِيمِ(23) Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. |
وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْئُولُونَ(24) Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. |
مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَ(25) Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna? |
بَلْ هُمُ الْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ(26) Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne. |
وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ(27) Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna. |
قَالُوا إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ الْيَمِينِ(28) Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)." |
قَالُوا بَل لَّمْ تَكُونُوا مُؤْمِنِينَ(29) Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba. |
وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَانٍ ۖ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَاغِينَ(30) "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka." |
فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَا ۖ إِنَّا لَذَائِقُونَ(31) "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne." |
فَأَغْوَيْنَاكُمْ إِنَّا كُنَّا غَاوِينَ(32) "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu." |
فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ(33) To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar. |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ(34) Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi. |
إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ(35) Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai. |
وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍ(36) Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci? |
بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ(37) Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni. |
إِنَّكُمْ لَذَائِقُو الْعَذَابِ الْأَلِيمِ(38) Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne. |
وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ(39) Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ(40) Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
أُولَٰئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌ(41) Waɗannan sunã da abinci sananne. |
فَوَاكِهُ ۖ وَهُم مُّكْرَمُونَ(42) 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa. |
فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ(43) A cikin gidãjen Aljannar ni'ima. |
عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَ(44) A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna. |
يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ(45) Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari. |
بَيْضَاءَ لَذَّةٍ لِّلشَّارِبِينَ(46) Farã mai dãɗi ga mashãyan. |
لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ(47) A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba, |
وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِينٌ(48) Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu. |
كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌ(49) Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye. |
فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ(50) Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna. |
قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٌ(51) Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)." |
يَقُولُ أَإِنَّكَ لَمِنَ الْمُصَدِّقِينَ(52) Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?" |
أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَدِينُونَ(53) "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?" |
قَالَ هَلْ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ(54) (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?" |
فَاطَّلَعَ فَرَآهُ فِي سَوَاءِ الْجَحِيمِ(55) Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim. |
قَالَ تَاللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِ(56) Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni." |
وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ الْمُحْضَرِينَ(57) "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)." |
أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ(58) "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba." |
إِلَّا مَوْتَتَنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ(59) "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?" |
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ(60) Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma. |
لِمِثْلِ هَٰذَا فَلْيَعْمَلِ الْعَامِلُونَ(61) Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa. |
أَذَٰلِكَ خَيْرٌ نُّزُلًا أَمْ شَجَرَةُ الزَّقُّومِ(62) Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm? |
إِنَّا جَعَلْنَاهَا فِتْنَةً لِّلظَّالِمِينَ(63) Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai. |
إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخْرُجُ فِي أَصْلِ الْجَحِيمِ(64) Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm. |
طَلْعُهَا كَأَنَّهُ رُءُوسُ الشَّيَاطِينِ(65) Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne. |
فَإِنَّهُمْ لَآكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ(66) To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta. |
ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبًا مِّنْ حَمِيمٍ(67) Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi. |
ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى الْجَحِيمِ(68) Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take. |
إِنَّهُمْ أَلْفَوْا آبَاءَهُمْ ضَالِّينَ(69) Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu. |
فَهُمْ عَلَىٰ آثَارِهِمْ يُهْرَعُونَ(70) Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa. |
وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ الْأَوَّلِينَ(71) Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu. |
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ(72) Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu. |
فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُنذَرِينَ(73) Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance. |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ(74) Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
وَلَقَدْ نَادَانَا نُوحٌ فَلَنِعْمَ الْمُجِيبُونَ(75) Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu. |
وَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ(76) Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba. |
وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُ هُمُ الْبَاقِينَ(77) Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa. |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ(78) Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe. |
سَلَامٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِي الْعَالَمِينَ(79) Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu. |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ(80) Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ(81) Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. |
ثُمَّ أَغْرَقْنَا الْآخَرِينَ(82) Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. |
۞ وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِ لَإِبْرَاهِيمَ(83) Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. |
إِذْ جَاءَ رَبَّهُ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ(84) A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. |
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَاذَا تَعْبُدُونَ(85) A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" |
أَئِفْكًا آلِهَةً دُونَ اللَّهِ تُرِيدُونَ(86) "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" |
فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ الْعَالَمِينَ(87) "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" |
فَنَظَرَ نَظْرَةً فِي النُّجُومِ(88) Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. |
فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٌ(89) Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." |
فَتَوَلَّوْا عَنْهُ مُدْبِرِينَ(90) Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. |
فَرَاغَ إِلَىٰ آلِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ(91) Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? |
مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ(92) "Me ya sãme ku, bã ku magana?" |
فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًا بِالْيَمِينِ(93) Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. |
فَأَقْبَلُوا إِلَيْهِ يَزِفُّونَ(94) Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. |
قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ(95) Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, |
وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ(96) "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?" |
قَالُوا ابْنُوا لَهُ بُنْيَانًا فَأَلْقُوهُ فِي الْجَحِيمِ(97) Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm." |
فَأَرَادُوا بِهِ كَيْدًا فَجَعَلْنَاهُمُ الْأَسْفَلِينَ(98) Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci. |
وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهْدِينِ(99) Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni." |
رَبِّ هَبْ لِي مِنَ الصَّالِحِينَ(100) "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne." |
فَبَشَّرْنَاهُ بِغُلَامٍ حَلِيمٍ(101) Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri. |
فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ السَّعْيَ قَالَ يَا بُنَيَّ إِنِّي أَرَىٰ فِي الْمَنَامِ أَنِّي أَذْبَحُكَ فَانظُرْ مَاذَا تَرَىٰ ۚ قَالَ يَا أَبَتِ افْعَلْ مَا تُؤْمَرُ ۖ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ اللَّهُ مِنَ الصَّابِرِينَ(102) To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri." |
فَلَمَّا أَسْلَمَا وَتَلَّهُ لِلْجَبِينِ(103) To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa. |
وَنَادَيْنَاهُ أَن يَا إِبْرَاهِيمُ(104) Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!" |
قَدْ صَدَّقْتَ الرُّؤْيَا ۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ(105) "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ الْبَلَاءُ الْمُبِينُ(106) Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. |
وَفَدَيْنَاهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍ(107) Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ(108) Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. |
سَلَامٌ عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَ(109) Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. |
كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ(110) Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ(111) Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. |
وَبَشَّرْنَاهُ بِإِسْحَاقَ نَبِيًّا مِّنَ الصَّالِحِينَ(112) Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. |
وَبَارَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَىٰ إِسْحَاقَ ۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ مُبِينٌ(113) Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). |
وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَارُونَ(114) Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. |
وَنَجَّيْنَاهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ(115) Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma. |
وَنَصَرْنَاهُمْ فَكَانُوا هُمُ الْغَالِبِينَ(116) Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya. |
وَآتَيْنَاهُمَا الْكِتَابَ الْمُسْتَبِينَ(117) Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni. |
وَهَدَيْنَاهُمَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ(118) Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِي الْآخِرِينَ(119) Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. |
سَلَامٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَارُونَ(120) Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ(121) Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ(122) Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai. |
وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ(123) Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَلَا تَتَّقُونَ(124) A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" |
أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ الْخَالِقِينَ(125) "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" |
اللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ(126) "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?" |
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ(127) Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã). |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ(128) Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ(129) Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe. |
سَلَامٌ عَلَىٰ إِلْ يَاسِينَ(130) Aminci ya tabbata ga Ilyãs. |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ(131) Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ(132) Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. |
وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ الْمُرْسَلِينَ(133) Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
إِذْ نَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ أَجْمَعِينَ(134) A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya. |
إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ(135) Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba). |
ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَ(136) Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. |
وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَ(137) Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. |
وَبِاللَّيْلِ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ(138) Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? |
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ(139) Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
إِذْ أَبَقَ إِلَى الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ(140) A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi. |
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ الْمُدْحَضِينَ(141) Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya. |
فَالْتَقَمَهُ الْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌ(142) Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. |
فَلَوْلَا أَنَّهُ كَانَ مِنَ الْمُسَبِّحِينَ(143) To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba, |
لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ(144) Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su. |
۞ فَنَبَذْنَاهُ بِالْعَرَاءِ وَهُوَ سَقِيمٌ(145) Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya. |
وَأَنبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍ(146) Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi. |
وَأَرْسَلْنَاهُ إِلَىٰ مِائَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ(147) Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka). |
فَآمَنُوا فَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَىٰ حِينٍ(148) Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci. |
فَاسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ الْبَنَاتُ وَلَهُمُ الْبَنُونَ(149) Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?" |
أَمْ خَلَقْنَا الْمَلَائِكَةَ إِنَاثًا وَهُمْ شَاهِدُونَ(150) Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce? |
أَلَا إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَ(151) To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa. |
وَلَدَ اللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ(152) "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne. |
أَصْطَفَى الْبَنَاتِ عَلَى الْبَنِينَ(153) Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza? |
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ(154) Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)? |
أَفَلَا تَذَكَّرُونَ(155) Shin, bã ku tunãni? |
أَمْ لَكُمْ سُلْطَانٌ مُّبِينٌ(156) Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne? |
فَأْتُوا بِكِتَابِكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ(157) To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya. |
وَجَعَلُوا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجِنَّةِ نَسَبًا ۚ وَلَقَدْ عَلِمَتِ الْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ(158) Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)" |
سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ(159) Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa. |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ(160) Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ(161) To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa, |
مَا أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَاتِنِينَ(162) Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi. |
إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ الْجَحِيمِ(163) Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm. |
وَمَا مِنَّا إِلَّا لَهُ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ(164) "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne." |
وَإِنَّا لَنَحْنُ الصَّافُّونَ(165) "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)." |
وَإِنَّا لَنَحْنُ الْمُسَبِّحُونَ(166) "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi." |
وَإِن كَانُوا لَيَقُولُونَ(167) Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa, |
لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنَ الْأَوَّلِينَ(168) "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko." |
لَكُنَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ(169) "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake." |
فَكَفَرُوا بِهِ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ(170) Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani. |
وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِينَ(171) Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni. |
إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنصُورُونَ(172) Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako. |
وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ الْغَالِبُونَ(173) Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya. |
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ(174) Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci. |
وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ(175) Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani. |
أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ(176) Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa? |
فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَاءَ صَبَاحُ الْمُنذَرِينَ(177) To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana. |
وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ(178) Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci. |
وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ(179) Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa. |
سُبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ(180) Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa. |
وَسَلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِينَ(181) Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. |
وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ(182) Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. |